Hakkin mallakar hoto Getty Images

Cibiyar kiyaye yaduwar cutuka ta Najeriya ta bayyana cewa kwamitin da ke yaki da cutar ebola za ta ci gaba da aiki domin shiryawa barkewar cutar.

Jami'an lafiyan sun furta hakan ne a matsayin martani kan hukuncin da Hukumar Lafiya Ta Duniya, WHO ta dauka na kadammar da dokar ta bacci kan ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

WHO ta dauki matakin ne bayan matsin lamba da ta fuskanta saboda yadda cutar ke bazuwa a sassan Congo da kuma makwabta, inda ake ganin kuma za ta yadu a kasashen duniya kamar yadda ta faru a baya.

Karkashin dokar, WHO ta bukaci kasashe su tsaurara binciken lafiya a kan iyakoki a matsayin matakan kariya ga barazanar cutar.

  • Najeriya ta yi shirin ko-ta-kwana kan cutar Ebola
  • Ebola ta kashe mutum 1000 a Congo
  • Bincike: Masu cutar Ebola na samin tabin hankali

Sai dai mai magana da yawun hukumar Dakta Margaret Harris, ta yi kira ga kasashen duniya da su kwantar da hankulansu ka da a samu irin rudanin da aka samu a baya.

Ta ce "Mun ga yadda a baya aka yi wa lamarin mummunar fahimta, abinda ya sa ya rikita jama'a.

"A cikin sanarwar da suka fitar mambobin kwamitin gaggawa na hukumar sun bayar da shawarwarri ga dukkan kasashen duniya da kada su rufe hanyoyin sufuri, da kawo tsaiko ga harkokin yau da gobe.

"Akwai abubuwa da dama da za a iya yi kuma wannan shi ne lokacin da ya kamata a fara aiki." in ji Dakta Margaret.

WHO ta kaddamar da dokar ta bacci kan ebola wacce ta riga ta kashe mutane da dama a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo bayan wani zaman tattaunawa da suka yi a ranar laraba.

Wannan zaman dai na zuwa ne bayan da WHO ta gano cewar cutar ta barke a birnin Goma da ke gabashin DRC, wanda ke da mazauna a kalla mutum miliyan 1.

A cewar WHO "Kwamitin gaggawa na hukumar ya shawrci duka kasashen duniya da kada su rufe hanyoyin sufuri, da kawo tsaiko ga harkokin yau da gobe."

Ministan lafiya a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Dakta Oly Illunga ya yi maraba da hukuncin kuma ya ce hukunci ba shi da bambanci da matakan da jami'an lafiya ke bi domin yaki da cutar.

Najeriya ita ce kasar Afirka mafi yawan mutane kuma ta ce a shirye ta ke don yakar cutar.

"Kwamitin da ke yaki da cutar ebola zai ci gaba da aiki domin yaki da kuma shiryawa cutar ta Ebola'', a cewar Cibiyar kiyaye yaduwar cutuka ta Najeriya.